<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>12</hymn_number>
<title>Allah Maɗaukaki, Sarki Madauwami LW12</title>
<lyrics>[V1]
 1) Allah Maɗaukaki, Sarki madauwami,
 Mu yabe ka.
 Kai ne Mahalicci, kai ne mai aminci,
 Kai ne mafifici har abada.

[V2]
 2) Mun taru wurinka, kai ne madogara,
 Mun yabe ka.
 Kai ne mai ƙaunarmu, kai ne mai fansarmu,
 Kai ne mai tsaronmu har abada.

[V3]
 3) Bayyana girmanka, nuna darajarka,
 Kusance mu.
 Tsarkake zukata, sauko da ikonka,
 Furta maganarka, ya Allahnmu.

[V4]
 4) Mallaki ƴaƴanka, ƙarfafa bayinka
 A duniyan nan.
 Yi amfani da mu, kwaƃi ragwancinmu,
 Mai da mu nan gaba manzanninka.</lyrics>
</song>